MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs_✍️* - (2024)

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs_✍️* - (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

_Tukwicine ga mahaifiyata, Hajiya mardiya Muhammad Bajini,Allah kareki ya miki sakamako da gidan Aljanna, ina sonki mamana❤️_

*Gargadi👂* *:* _Banyi littafina don cin mutincin kowa ba, nayi ne don kawo gyara, hade da nusar da wasu daga cikin matan hausawa, don haka duk wacce labarina yayi dai² da ita akasi aka samu, da fatan zamu gyara._

*_ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ_*

_______________________________

Tun daga madaidaicin tsakar gidan ake jiyo hiransu, yayin da suke yi suna k’yatatawa da dariya, kutsa kai nayi parlourn na shige, madaidaicin parlour ne mai d’auke da saitin kujeru madaidaita, sai dan mini plasma tv da receiver, daga gefe kuma fridge ne mai yanka, sama da kasa, Amina kenan da yaranta su hudu, maza biyu, mata biyu, danta na fari shine Abdullahi mai shekara 17, sai mai bi masa Asma’u mai shekara 15, sannan sai munnira mai shekara 13, sai autanta Ahmad mai shekara goma, hiransu suke cikin farin ciki da kwanciyar hankali, yayin da Tv ke ta faman aiki, sai dai hankalinsu ba ya wurin kwata².

Karfe tara dai² ya shigo gidan, inda ya gunguro mashin dinsa ciki tare da kulle kofar gidan da mukulli, daukan ledojin dasuke basket din gaban mashin din yayi, sannan ya nufo parlourn bakinsa dauke da sallama, sai dai basu masan yana yi ba, sai da ya kuma yi da karfi, cikin dariya Amina da yaranta suka amsa tare da masa sannu da zuwa.

Alhaji usman kenan, miji ga Amina, uba kuma gasu Abdullahi, fari ne tas dashi dan gayu, don ko yanxu sanye yake da blue jeans dinsa, sai blue Tshirt dinsa mai layi² da black cover shoe a ‘kafarsa, wacce ke d’auke da safa, d’an kasuwane anan kasuwar sabon garin zaria, yana saida atampopi da sauran kayan mata, yana da rufin asirinsa dai² gwargwardo, a shekaru zai kai shekara 40, amma inka kallesa zaka d’auka bai wuce shekara 30 ba, saboda yanda yake da mugun son gayu, tsafta, ga gyara, ba za kace shi ya haifi su Abdullahi ba, zaka fi kawowa k’annansane.

Shiga yayi yana mai amsa sannu da zuwansu, leda d’aya ya ajiye musu, sannan ya nufi bedroom da d’ayar ledar, zama yayi bakin italian bed d’in dake d’akin, yana mai bin dakin da kallo, yanda ya fita yabar shi da safe haka ya same sa ba tare da an gyara ba, sai ma ‘karin datti da ya samu, kan gadon kuma an gibza kaya da alamun daga igiyar shanya aka d’ibosu ba a ninke ba, d’an tsaki yaja, yana mai ‘bata rai, mik’ewa yayi ya hau cire kayansa, sai da ya rage daga shi sai boxer, sannan ya shige toilet d’in da ke cikin d’akin.

A can parlour kuma, Amina ce ta dubi Asma’u tare da cewa “daughter miko min ledar nan inga mai Abbanku ya kawo” ta k’arasa magana tana nuna mata ledar da hannu.

D’aukowa tayi ta kawo mata, tana mai fadin “ummi kamar kaza ce fa don naji kamar k’amshinta nake ji”.

Karba tayi ta bude, sannan tace “Aiko kaza ce, kamar yasan kwadayinta nake ji, an kwana biyu ba a hadu ba, kusa hannu muci” ta fadi tana mai ijiye ledar akan dan center table din dake gabansu, take duk suka zuba hannu suka fara ci, suna mai ci gaba da hirarsu.

Ko da ya fito wanka yaga bata a dakin sai daja tsaki, had’e da fad’in “Ai dama nasan shigowarta badai yanxu ba, tunda mai hali baya barin halinsa, sai anjima ta shigo tana ta wata mik’a, sunan tana jin bacci”.

Mai ya shafa had’e da fesa turare masu kamshi, sannan ya d’auko wasu kayan bacci masu taushi farare tas ya saka, zama yayi bakin gado yana mai kwala mata kira “Amina !,Amina!!”.

Dai² lokacin da taji kiransa tana mai gwagwiyar cinnyar kaza😋, hakan yasa sai da ya kira so uku ta amsa tare da cewa “ina zuwa”.

Kallon munnira tayi tana mai cewa “nasan ya fito wanka , maganar Abinci ce, ke munnira yi sauri ki shiga kitchen ki zuba ma Abbanku Abinci a plate ki kai masa d’aki, da alamar ya shiga kenan ba zai fito ba”.

“To ummy” amsawar munnira tana mai tashi, yayin da su kuma suka ci gaba da cin kazarsu.

Shinkafa da miya ce munnira ta zubo a plate, duk ta dunkule, sannan ta bud’e fridge ta d’auki pure water d’aya a hannu ta nufi bedroom d’in, da sallama ta shiga, sannan ta dire plate d’in abincin a gabansa, had’e da ajiye masa ruwan a gefensa tana mai fad’in “Abba ga Abincinka nan inji ummy” ta karasa magana tana mai mik’ewa ta fice a dakin.

Kallo yabi abinci dashi cike da takaici, sannan ya d’auka ya dan yamutsa ya kai bakinsa, mutsa fuska yayi yana mai had’iyewa da ‘kyar, mai da abincin yayi ya ijiye sannan ya d’auki ruwa ya sha.Ture kayan kan gadon yayi gefe, sannan ya kwanta ranshi bace.

Can parlourn kuma ci gaba da dinnersu suka yi da kaza, aka ci aka tsotse k’ashin, sannan suka wanko hannu, kowannesu cikin yaran ya nufi d’akin kwananshi, (wanda d’akin mazan ke tsakar gida, na matan kuma na cikin parlourn kusa da kitchen )suna masu fadin “ummy sai da safe”, da murmushi ta rakasu tana mai fadin “Allah bamu Alkhairi”.

Tashi tayi ta rufo kofar parlourn sannan ta kashe Tv da kwayayen wuta, ta nufi bedroom d’insu.

Da sallama ta shiga d’akin, yayin da shi kuma yake kwance yana ‘kar’kad’a ‘kafa, yana ‘kare mata kallo, sanye take da wata burgujejiyar Tshirt, sai wani kod’add’en zani, da wata hula akanta, ‘Karasowa tayi tana mai kallon abincin tare da tambayarsa ” Abban yara baka ci Abincin bane?”.

“Ban ci ba”ya fadi rai a bace.

Tsaresa tayi da ido tana mai tambayar “saboda me?”.

A fusace yace “tsakani da Allah Amina wannan abincin ne zan iya ci, gashi da sanyi, ga miyar tayi tsami”.

“Eyyah, ni nama manta wallahi, kayan miyanne keda masifar tsami, nima sai da na kai bakina na ji, kuma Asma’u tace min ta saka kanwa da baking powder amma tsamin bai fita ba, muma haka muka ci, sai hakuri” ta fadi kanta tsaye.

Binta da kallo yake cikin b’acin rai, yana mai karkad’a k’afa, sannan yace “kuma da kika ji haka, kika kasa mai data wuta ki kara mata kanwar, sannan kuma shinkafar ma kula ta gagara a sakamin, wai don Allah Amina ke wace irin mata ce, abinci ba taste, ji bedroom shima babu gyara, ga kaya a kan gado”.

Itama ‘bata rai tayi tana mai fad’in “wai me yasa hakane Abban yara?, duk kok’arin da nake yi baka gani, d’aki munnira na sa gyarawa tun azahar bata yiba, kaya kuma daga shanya aka kwasosu nace su zuba a nan kafin a ninke”.

Girgiza kai kawai yayi, sannan yace ” naji wannan, ina tawa rabon kazar?”.

“Kaza!, chab wallahi mun cinye ni da yaranka” tayi magana tana mai yarfar da hannu .

Wata hararar ya zuba mata tare da cewa “kazar duka biyu, kice kun cinye ke da yarana, wai don Allah mai yasa hakane?, Amina shekaranmu goma sha tara da aure, amma har yau baki son ki daraja miji ba, baki son ki kula dashi ba, tunda kika yi ‘ya’ya shike nan kika zubar da kulawarki gareni, don Allah jibe ki, jibi kayan jikinki, duk kinbi kin tsofar da kanki” ya kare zancen yana mai nuna ta da hannu.

Kada baki tayi tace” ai tsufa ko ban tsofar da kaina ba na tsufa, in ajiye Abdullahi da Asma’u, sannan kace wani na tsofar da kaina, kai dai da kake mai da kanka baya, sai kaje kayi tayi, amma ai don tsufa mun tsufa tunda mun kusa jikoki”.

Binta yayi da kallo yana mai jijjiga kai, tsaki yaja ya gyara kwanciyarsa yana mai juya mata baya,itama matsar da kayan can gefe tayi, sannan ta kashe haske ta kwanta…..

Asuba ta gari hajiya Amina mata ga Alhaji usman dan gaye.

*_This is just the beginning, shin kun fara hango halayen matar bahaushe ko?_*

*_Fateeyzah mbs✍️_*

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs_✍️* - (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Twana Towne Ret

Last Updated:

Views: 6015

Rating: 4.3 / 5 (64 voted)

Reviews: 87% of readers found this page helpful

Author information

Name: Twana Towne Ret

Birthday: 1994-03-19

Address: Apt. 990 97439 Corwin Motorway, Port Eliseoburgh, NM 99144-2618

Phone: +5958753152963

Job: National Specialist

Hobby: Kayaking, Photography, Skydiving, Embroidery, Leather crafting, Orienteering, Cooking

Introduction: My name is Twana Towne Ret, I am a famous, talented, joyous, perfect, powerful, inquisitive, lovely person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.